Rahoton ya ce, yunkurin raya bil Adamu a kasashen da ke yankunan Asiya da tekun Fasific cikinsu har da kasar Sin ya kawo babban canji ga dangantakar kasa da kasa. Rahoton ya jinjinawa fasahohin da Sin ta samu wajen yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje, haka kuma, ya jaddada tasirin da karuwar tattalin arzikin Sin ya kawo wa kasashe masu tasowa, musamman wadanda suka kulla dangantakar abokantakar cinikayya da kasar Sin.
Haka kuma, rahoton ya yaba wa aikin saka jari da kasar Sin ke yi ya sa kaimi ga ci gaban tattalin arzikin kasashen Afirka, musamman ma, Sin ta taimakawa kasashen Afrika wajen daukaka matsayin kayayyakinsu.
Rahoton ya ce, manyan tsare-tsare da Sin take bi domin kafa zamantakewar al'umma mai jituwa, sun nuna muhimmanci wajen samar da daidaito a zamantakewar al'umma, kuma su kasance abun koyi ga tarin kasashe masu tasowa.(Bako)