Madam Hua ta kara da cewa, Sin ta yi Allah wadai da 'yan adawa na kasar Siriya kan tsare ma'aikatan kiyaye zaman lafiya na M.D.D. kuma ta bukaci da a sake su nan take, ba tare da gindaya wasu sharudda ba. Haka kuma, Sin ba za ta amince da dukkan hare-hare da barazanar da za a kawo wa rundunar sojojin kiyaye zaman lafiya ta M.D.D ba, haka kuma kasar Sin ta bukaci bangarorin da abin ya shafa da su dauki kwararan matakai, don tabbatar da tsaron ma'aikatan kiyaye zaman lafiya na M.D.D.
Bisa labarin da aka bayar, an ce, shugaban karba-karba na kwamitin sulhu na M.D.D na wannan wata, kuma zaunannen wakilin kasar Rasha da ke M.D.D. Vitaly Churkin ya bayyana cewa, kwamitin sulhu na M.D.D. ya yi Allah wadai da 'yan adawa na Siriya kan tsare sojoji masu kiyaye zaman lafiya na M.D.D kimanin 20 a kusa da yankin Golan, kuma ya bukaci su da a sake su nan take.(Bako)