Jami'in kula da harkokin jin kai na MDD da ke Somaliya Mark Bowden ya fada cikin wata sanarwar da aka bayar a ranar Jumma'a da dare cewa, tallafin jin kai da aka samar a yankunan Bay, Bakool da Lower Shabelle da suka fama da yunwa ya yi tasiri matuka, al'amarin da ya fitar da wadannan yankuna daga matsalar yunwa.
Ko da yake a cewar wasu alkaluma na baya-bayan nan da sashen nazarin samar da abinci da abinci mai gina jiki (FSNAU),da tsarin bayar da gargadin barkewar yunwa a kudancin Somaliya suka tattara,ana ci gaba da fuskantar yunwa a wasu sassan shiyar tsakiyar Shabelle, yankunan da aka tsugunar da mutanen da yunwa ta daidaita a Mogadishu babban birnin kasar da kuma yankin Afgooye.
Galibin yankunan kudancin Somaliya na kasancewa a kan gaba a duniya wajen fama da matsalar abinci mai gina jiki da mace-macen yara.
A farkon wannan shekara ne fari mai tsanani ya mamaye kusurwar Afirka, al'amarin da ya haddasa karancin abincin da ya yi sanadiyar rayukan dubban mutane a Somaliya kana ya cusa sama da mutane miliyan 3.2 cikin matsalar yunwa.
Wani kokarin tallafi da aka bayar ya taimaka wajen kaiwa ga mutane miliyan 2.2 da lamarin ya shafa, inda aka basu taimakon abinci da ruwa.
Sanarwar ta ce hukumar kula da harkokin jin kai za ta kaddamar da gidauniyar neman taimako a farkon wannan wata don samar da taimakon da ya dace da Somaliya a 2012.(Ibrahim)