Hedkwatar kasar Nijar, Niamey za ta karbi bakunci wasannin jami'o'in kasashen dake cikin kwamitin jituwa na "Conseil de l'Entente" da ake fada haka da Faransanci wato CE dake kunshe da kasashen Benin, Burkina-Faso, Cote d'Ivoire, Nijar da Togo daga ranar 25 zuwa 30 ga watan Maris, a cewar hukumomin birnin Niamey. Burin da ake son cimmawa a wannan karo, a cewar shugaban kwamitin shirya wasannin Niamey mista Ide Moussa, shi ne na farko da aka sake kawo azama ga tsarin shirye-shirye bayan wani yanayin tafiyar hawainiya tun lokacin wasannin Bamako a shekarar 2005, lokacin da aka kafa wani tsarin musanya da karfafa dangantakar abokantaka da sada zumunci tsakanin malamai da dalibai na dukkan jami'o'i, da kuma wani tsarin samar da yanayin cudanya, musanya da bunkasa zaman jituwa tsakanin dalibai, masu horo da shugabannin wadannan jami'o'in gwamnati. Haka kuma wannan haduwa ta kasance wata hanyar kirkiro da ba da kwarin gwiwa ga wadannan jami'o'i bisa muhimmancin gafartawa juna, zaman lafiya da kuma fahimtar juna, taimakon juna, aiki tare, kafa tsarin musanya tsakanin jami'o'i da fadada manufar baiwa dalibai damar shirya muhamman wasannin motsa jiki da al'adu na tsakaninsu. (Maman Ada)