'Yan sandan birnin Boston da masu shirya gasar sun tabbatar da cewa, an yi fashewar boma-bomai sau biyu a wurin dake dab da karshen layin gasar. Shugaban 'yan sandan birnin Ed Davis ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar cikin gaggawa a wannan rana da yamma cewa, bom na uku ya fashe ne a dab da dakin karatu na JFK na Boston, amma 'yan sandan ba su tabbatar da cewa, ko fashewar bom din na uku na da nasaba da fashewar boma-bomai biyu da aka samu kafin shi ba.
Bisa labarin da kafofin watsa labaru na kasar Amurka suka bayar, an ce, 'yan sandan sun gano boma-bomai biyu na daban a dab da wurin abkuwar lamarin, kuma ana kokarin kawar da su.
Don tinkarar lamarin, 'yan sandan birnin na Boston sun sanar da hana zirga-zirgar jiragen sama a yankin da lamarin ya faru. Kana wasu manyan biranen kasar kamar New York da Washington D.C sun dau matakan musamman a wuraren da aka fi samun yawan mutane don magance abkuwar lamarin kamar hakan.
A wannan rana kuma, shugaban kasar Amurka Barack Obama ya yi wani jawabi a fadar shugaban kasar wato White House, inda ya yi alkawarin bin bahasin wannan lamari tare da kama masu hannu a lamarin. Kana ya ce, za a kara daukar matakan da suka wajaba don tabbatar da zaman lafiya a kasar, da kuma yin bincike kan dalilin abkuwar lamarin. (Zainab)