in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yaki da rashin hukunci ya zama wajibi a kasar Cote d'Ivoire
2013-03-20 14:20:08 cri

Yaki da rashin hukunci ya kasance mafi dacewa ga kasar Cote d'Ivoire bisa turbar zaman lafiya, in ji wani masani mai zaman kansa game da matsalar 'yancin 'dan adam a kasar Cote d'Ivoire a birnin Geneva.

Cigaban gina wata manufar siyasa ta kasa bisa matuntawa da bunkasa 'yancin 'dan adam na fuskantar kalubale na rashin hukunci masu laifi da kuma rashin adalci ta fuskar shari'a, in ji mista Doudou Diene, wani kwararre mai zaman kansa, a yayin wani zaman taro karo na 22 na kwamitin 'yancin 'dan adam dake gudanarwa yanzu haka a birnin Geneva.

Yaki da rashin hukunci na bisa hanya, sai dai har yanzu wannan lokaci bangare guda ake ma bita da kulli kawai, musammun ma kan magoya bayan tsohon shuagaban kasar Laurent Gbagbo. Muhimmin abu shi ne kama wadanda suka aikata munanan ayyukan cin zarafin 'dan adam ba tare da nuna bambanci ba ta fuskar siyasa, kabila, yanki ko addini, in ji mista Diene.

A cewarsa, matsalar 'yancin 'dan adam a kasar Cote d'Ivoire na ta'allaka da cigaban demokaradiyya, tattalin arziki da al'umma da aka dauka da kuma muhimman kalubale da suka fito daga dogon tarihi, tunani da siyasa na wannan rikici, munanan ayyukan kuntatawa na cin zarafin 'dan adam cikin dogon lokaci da kuma yunkurin gurbata tsaro. Dalilin haka ne kasar Cote d'Ivoire take bukatar taimakon taka tsantsan na gamayyar kasa da kasa domin karfafa ciagaban demokaradiyya, adalci cikin shari'a, tabbatar da 'yancin 'dan adam dake cike da al'adu masu daraja na zaman jituwa, in ji mista Doudou Diene. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China