in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar adawa ta Masar ta yi kiran zanga-zanga dangane da tsare masu gwagwarmayar siyasa
2013-03-28 11:01:14 cri

Babbar kungiyar adawa ta kasar Masar ta yi kira ranar Laraba na yin zanga-zangar lumana a hedkwatar babban ofishin tuhumar jama'a dangane da cafke wasu 'yan gwagwarmayar siyasa.

Kungiyar National Salvation Front ta ki amincewa da shige gona da iri a harkar mulki da hukumar tuhumar jama'a ke yi wajen warware rikicin siyasa da masu adawa da gwamnati.

Ta kuma yi kiran aiwatar da shari'a da kotu ta yanke na soke nadin da shugaba Mohammed Morsi ya yi wa Talaat Ibrahim a matsayin babban mai gurfanar da jama'a.

Kungiyar ta dora laifin asarar rayuka da aka fuskanta kwanan nan a kasar Masar kan shugaban kasar tare da yin gargadi dangane da kaucewa ka'idoji na mulki ko kuma cin zarafin hukumar shari'a.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, ba za ta amince da mulkin danniya ba wanda ta alakanta da jawabi da shugaba Morsi ya yi kwanan nan dake barazanar daure masu adawa.

Ta kuma bayyana cafke masu gwagwarmayar siyasa guda biyar da hukumar gurfanar da jama'a ta yi da cewa, aiwatar da barazana da shugaban kasar ya yi ne.

A ranar Litinin ne hukumar gurfanar da jama'a ta kasar Masar ta bayar da takardun izinin kamowa da kuma hana wasu masu gwagwarmayar siyasa su biyar fita waje, dangane da zargin cewa, sun tunzura jama'a su ta da hankali a wajen hedkwatar kungiyar Muslin Brotherhood dake Alkahira.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China