in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Boko Haram ta ce, ba za ta saki 'yan Faransa ba muddin ba'a sake mambobinta ba
2013-03-22 10:09:18 cri

Kungiyar Boko Haram ta Najeriya ta yi bayani ta hotunan bidiyo da aka nuna a gidan talbijin din kasar Faransa, iTELF ranar Alhamis cewa, kungiyar ba za ta saki iyalan 'yan kasar Faransa ba, muddin 'yan kungiyar Boko Haram na tsare.

Mai satar mutanen ya ce, suna rike da su ne saboda hukumomin kasar Najeriya da Kamaru sun cafke iyalansu kuma suna gana masu azaba, kana ba su san irin halin da ake tsare da su ba.

An saki hotunan bidiyon ne kwanaki uku bayan wanda aka nuna a baya inda mahaifin iyalan 'yan kasar Faransa ya yi bayani kan wahalar rayuwa bayan da 'yan kungiyar suka sace su.

Mahaifin ya bukaci a saki mambobin kungiyar dake tsare domin shi ma nasa iyalansu samu 'yanci.

Ana kyautata zaton cewa, mambobin kungiyar Boko Haram ne suka sace iyalan Faransa da 'ya'yansu hudu 'yan shekaru tsakanin biyar zuwa goma sha biyu da kuma manya guda uku ranar 19 ga watan Fabrairu a garin Dabanga dake arewacin kasar Kamaru a hanyar kan iyakar kasar da Najeriya.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China