Babban magatakardar MDD Ban Ki-moon a ranar Laraban nan 24 ga wata ya ce, ya ji dadin da aka fara tattauna yadda za'a samu zaman lafiya tsakanin gwamnatin kasar Sudan da kungiyar 'yan tawaye a birnin Addis Ababa na kasar Habasha.
A cikin wata sanarwar da ta fito daga ofishin kakakinsa, Mr. Moon ya ce, ya samu kwarin gwiwwa da aka fara wannan tattaunawa kai tsaye tsakanin gwamnatin na Sudan da na 'yan tawayen SPLM bangaren arewacin kasar a kan sharuddan kwamitin zaman lafiya da tsaro na kungiyar tarayyar kasashen Afrika AU da kuma kwamitin tsaro na MDD.
Wannan tattaunawar da gwamnatin na Sudan ta yi da kungiyar 'yan tawayen SPLM bangaren kudancin Kordofan da jihohin Blue Nile na kasar a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha, ya bayyana aniyar dukkan bangarorin na samar da mafita a kan rikicin da suke yi, in ji sanarwar.
Don haka, babban magatakardar ya yi kira ga dukkan bangarori da su amince da dakatar da duk wani gaba a tsakaninsu nan take domin a samar da kafar da za'a kai taimakon kayayyakin jin kai ga fararen hula da ke zaune a yankunan da ake bata kashi, sannan kuma su samar da yanayi mai kyau da za'a samar da dauwamammen siyasa mai inganci da zai maye gurbin tashin hankalin da ake fuskanta.(Fatimah)