Mahukuntan kasar Sudan sun yi watsi da dukkanin wani kurarin da kungiyar nan ta 'yan tawayen SPLM tsagin arewacin kasar suka yi, na cewa, za su kaddamar da sabbin hare-hare, ciki hadda wanda suka ce za su kai Kadogli, babban birnin jihar Kudancin Kordofan.
A baya bayan nan ne dai rundunar 'yan tawayen ta gabatar da wannan barazana, tana mai umartar fararen hula da su fice daga wannan yanki, domin gudun abin da ka iya aukuwa. Wannan barazana dai na iya yawaita adadin al'ummomin da ke kauracewa gidajensu, da karin wahalhalu da mutanen wannan yanki na Kadogli, wanda hakan shi ne burin wannan kungiya, a cewar ministan harkokin wajen kasar ta Sudan.
Wata sanarwa da ta fito daga ofishin ministan ta kara da cewa, wannan ikirari da kungiyar ta SPLM reshen arewaci ta yi, laifi ne, sun kuma yi hakan ne domin tada zaune tsaye, tare da dada kuntatawa al'ummar dake wannan yanki. Har ila yau sanarwar ta bukaci hukumomin kasa da kasa, da su dauki matakin dakile wannan barazana da 'yan tawayen ke yi.
Bugu da kari, sanarwar ta ce, ba da mafaka ga jagororin 'yan tawayen da wasu kasashe ke yi, musamman wadanda suka ki amincewa da batun sulhu, na ba su damar samun karfi ta fuskar siyasa da karfin soji, wanda hakan ya janyo aukuwar laifukan ta'addanci da suke yi a kasar ta Sudan.
Wani labarin ma mai alaka da wannan na nuna cewa, a ranar Juma'ar da ta gabata, wasu mutane 10 sun rasa rayukansu, sakamakon fashewar wani bam, da 'yan tawayen suka dasa.
Wannan dai yanayi na dauki ba dadi, tsakanin dakarun gwamnati da na 'yan tawayen da suka kulla abota, da ragowar rundunonin 'yan tada kayar baya a jihar Kudancin Kordofan, na wakana ne tun daga shekarar 2011, lamarin da kuma mahukuntan Sundan ke dangantawa da tallafi da SPLM din ke samu daga Sudan ta Kudu, kasar da ta ce sam, ba ta da hannu cikin wannan zargi da ake mata, yayin da ita kuma Sudan din ke cewa, ba za ta zauna teburin shawara da kungiyar ta SPLM ba, har sai ta katse alakarta da Sudan ta Kudu.(Saminu)