in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tuni kungiyar 'yan uwa Musulmi dake Masar ta samu halasci, in ji lauyanta
2013-03-21 10:20:23 cri

Biyowa bayan wani rahoto da ofishin babbar kotun koli kan harkokin mulki ta kasar Masar ya fitar ranar Laraba 20 ga wata, wanda ke nuni ga bukatar rushe kungiyar nan ta 'yan uwa Musulmi dake kasar, lauyan kungiyar Abdel-Moniem Abdel-Maqsoud, ya ce, rahoton ba shi da wani tushe.

Lauyan kungiyar ya kara da cewa, tuni wannan kungiya da yake wakilta ta samu cikakken halasci a kasar ta Masar. Cikin wata sanarwar da aka sanya a shafin yanar gizon reshen siyasar kungiyar, Abdel-Maqsoud ya ce, kungiyar na ganin bayyana wannan matsayi nata a baya, ba shi da wani muhimmanci, don haka ba su yayata batun samun halascin nata ba, amma a cewarsa, hakan ba ya nuna rashin halascin, kamar yadda wancan rahoto ke kokarin nunawa.

Daga nan sai lauyan ya tuhumi fidda wannan rahoto a wannan gaba, yana mai cewa, hakan na da hadari, idan aka yi la'akari da cewa, lokaci ne da ake ta kiraye-kiraye na rusa kungiyar, tare da kaiwa helkwatarta hare-hare.

Ita dai wannan kungiya ta 'yan uwa Musulmi ko "Muslim Brotherhood" ita ce a kan gaba, wajen marawa shugaban kasar mai ci Mohammed Morsi baya, wanda karkashin inuwar sashenta na siyasa wanda ya jagoranta a baya, wato "Freedom and Justice Party", ya samu kaiwa ga nasarar lashe babban zaben kasar da ya gabata.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China