Dan Faransa da ake garkuwa da shi a Najeriya ya bayyana wahala da suke sha cikin bidiyon da Boko Haram ta nuna
Wani mutum wanda ake ganin cewa shi ne shugaban iyalan nan ‘yan kasar Faransa da ake garkuwa da su a Najeriya, cikin wani sabon hoton bidiyo da aka nuna ya ce, suna cikin mawuyacin hali, in ji rahotanni da kafofin labaran Faransa suka bayar ranar Litinin.
Bafaranshen mai suna Moulin Fournier ya bayyana cewa, sun yi kwanaki 25 a tsare, kuma suna rayuwa cikin mawuyacin hali.
Ya ci gaba da cewa, ba su da kuzari kuma sun fara rashin lafiya sakamakon hakan, in ji kafar watsa labaran talbijin ta BFMTV.
Yana mai kira ga jakadan Faransa a Najeriya da ya yi dukkan kokarin tabbatar da ganin an saki iyalan.
Wannan shi ne hoton bidiyo na biyu na iyalan Faransa da aka nuna bayan na farko da aka nuna ran 25 ga watan Fabrairu a kafar intanet ta YouTube.
Wadanda suka sace su suna barazanar cewa, za su kasha su muddin jami’an kasar Najeriya da na kasar Kamaru ba su saki mayakan Islama ba.
A karshen makon da ya wuce, ministan harkokin waje na Faransa Laurent Fabius ya kai ziyara a Kamaru, a kokarin da ake na ganin an saki ‘yan Faransa da ake garkuwa da su a Najeriya.(Lami)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku