in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi ya bayyana tabbacin farfadawo daga mummunan girgizar kasar da ta faru a yankin kuda maso yammacin kasar
2013-04-22 20:42:15 cri
A ranar Litinin ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana cewa, ana gudanar da aikin ceto a yankin da girgizar kasar da ta faru a yankin kudu maso yammacin kasar yadda ya kamata kuma al'ummar kasar za su jure irin matsalolin da bala'in ya haifar.

Xi Jinping ya ce al'ummar kasar Sin za su iya sake gina gidajensu karkashin shugabancin JKS da gwamnatin kasar Sin tare kuma da taimakon al'ummar kasa da kasa.

A ranar Asabar da safe ne wata girgizar kasa mai karfin maki 7 bisa ma'aunin richet ta abkawa lardin Sichuan da ke kudu maso yammacin kasar Sin, inda mutane a kalla 188 suka mutu kana kimanin miliyan 1.5 bala'in ya shafa sun ji raunuka.

Shugaban na Sin ya bayyana godiya bisa juyayi da goyon bayan da al'ummar kasa da kasa suka nuna kan wannan lamari, lokacin da ya karbi takardar aikin sabbin jekadun kasashen waje guda 9 da aka turo zuwa nan kasar Sin. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China