in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta sake nanata alkawarin da ta dauka cewa ko kusa ba za ta zama ta farko wajen yin amfani da makaman nukiliya ba
2013-04-23 16:12:33 cri
A ranar 22 ga wata, a birnin Geneva, direktan sashen kayyade yawan karfin soja na ma'aikatar kula da harkokin wajen kasar Sin Pang Sen ya bayyana cewa, kasar Sin ta tsaya haikan game da manyan tsare-tsare na kasar wajen amfani da nukiliya domin kare kanta, kuma ta cika alkawarin da ta dauka cewa, ko yaushe kuma kowane irin yanayi ba za ta zama ta farko wajen yin amfani da makaman nukiliya ba, kana kuma, ta dauki alkawarin kaucewa kawo barazana ga sauran kasashe ko yankunan da ba su da makaman nukiliya.

A wannan rana, a fadar Palace of Nations da ke birnin Geneva, an yi muhawara a gun taron share fage karo na biyu domin babban taron dudduba yarjejeniyar hana yaduwar makamai a karo na 9, shugaban tawagar kasar Sin Pang Sen ya bayyana cewa, gwamnatin Sin ta tashi tsaye bisa yunkurin rage makaman nukiliya a duniya, da kuma barazanarsu a duniya, don kafa wata duniyar babu makaman nukiliya, haka kuma Sin ta kan rage yawan makaman nukiliya bisa la'akari da bukatunta, kuma ba ta taba jibge makaman nukiliya a sauran kasashe ba, kuma ba ta taba shiga kowane irin takara don mallakar makaman nukiliya ba, nan gaba ma haka za ta yi.

Pang Sen ya ce, kasar Sin ta sauke nauyin da ke bisa kanta don hana yaduwar makaman nukiliya a duniya, kuma ta yi tsayuwar daka ga kin yaduwar makaman nukiliya ta kowace hanya, kana kuma, an kafa wani tsarin doka a cikin kasar wajen hana fitar da makaman nukiliya zuwa sauran kasashen duniya bisa ka'idar kasa da kasa. Haka kuma, kasar Sin ta nace kan warware batun nukiliya na zirin Koriya ta hanyar yin shawarwari, don cimma burin kawar da makaman nukiliya a zirin Koriya, don tabbatar da zaman lafiya da karko a yankin arewa maso gabashin kasashen Asiya.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China