in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Najeriya ya bude kamfanin sarrafa karafa
2013-04-19 10:53:28 cri






 

 

Shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan ya kaddamar da kamfanin sarrafa karafa na biliyoyin dalar Amurka wanda kuma ake ganin shi ne mafi inganci da girma irinsa a nahiyar Afirka baki daya.

Shugaban na Najeriya ya bude kamfanin wanda na zaman kansa ne mallakar kamfanin sarrafa karafa na Hong Kong, WEMPCO, a garin Magboro dake kudu maso yammacin jihar Ogun a kasar.

Da yake gabatar da jawabinsa, shugaba Goodluck Jonathan ya jadadda cewa, kamfanin sarrafa karafan zai taimaka matuka wajen samar da aikin yi ga matasan kasar, kana zai taimaka wajen bunkasa harkokin masana'antu.

Za'a iya sarrafa karafa tan dubu dari bakwai kowace shekara, kana ana iya fadadashi da karin tan dubu dari uku, kuma ana sa rai cewa, za'a fara aiki a kamfanin a cikin watanni uku na karshe na shekarar 2013.

Lewis Tung wanda shi ne babban manajan darekta na kamfanin WEMPCO ya ce, kamfanin a shirye yake ya karbi kayayyakin sarrafawa daga masana'antu, inda ta hakan za'a ja hankalin masu zuba jari a fannoni daban daban a wannan harka.

Ya ci gaba da cewa, kamfanin tare da abokan hadin gwiwa na kasashen Sin, Amurka, Jamus da Japan a shirye yake ya taimakawa kasar Najeriya a inda take da koma baya a fuskar fasaha.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China