in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministar Najeriya ta zamo shugabar majalisar gudanar da shirin muhalli na MDD
2013-04-16 10:43:57 cri

An zabi ministar gidaje, filaye da bunkasa birane ta kasar Najeriya Amal Pepple ranar Litinin a matsayin sabuwar shugabar majalisar gudanarwa ta hukumar shirin muhalli na MDD da ake kira UN-Habitat, jiko na 24.

Pepple ta maye gurbin Albert Nsengiyumva, ministan ababan more rayuwa na kasar Ruwanda, wanda shi ne shugaban majalisar a jiko na 23.

Darektan hukumar shirin UN-Habitat Dr. Joan Clos ta bayyana cewa, taron shirin mataki na uku, wanda za'a gabatar a shekarar 2016 zai samar da wata kyakyawar damar nazarin ajandar birane ga masu ruwa da tsaki.

Sabon shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta shi ne ya bude taron na tsawon mako daya. Majalisar gudanarwar na ganawa bayan shekara biyu-biyu, don nazarin ayyukanta da dangantaka da abokan hadin gwiwa.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China