in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar UNHCR a Najeriya ta samar wa 'yan gudun hijirar Laberiya fasfo na ECOWAS
2013-04-11 10:24:08 cri

Ofishin hukumar MDD mai lura da 'yan gudun hijira UNHCR, ya samar wa 'yan gudun hijirar kasar Laberiya fasfo a Najeriya, na kasashe mambobin kungiyar ECOWAS.

Babbar jami'ar ofishin a jihar Legas dake kudancin kasar, Josephine Smith ce ta bayyana hakan ga manema labaru ranar Laraba 10 ga watan nan, Smith ta kara da cewa, cikin 'yan gudun hijirar Laberiya 925 da suka nuna sha'awar zama a Najeriyar, hukumar ta samu fasfo na shaidar damar zama a kasar ga mutane 395, yayin da ake dakon karin na mutane 530.

A cewarta, hukumar ta UNHRC, na tsara wani shirin da zai ba da dama cikin sauri, ga masu neman mafakar siyasa a Najeriya, daga kasashen Congo, da Chadi, da Camaru da kuma kasar kwadebuwa.

A watan Janairun da ya gabata ne dai hukumar lura da 'yan gudun hijirar ta MDD, ta bayyana mai da kimanin mutane 150,000 zuwa Laberiya, bayan sun shafe shekaru 23 a Najeriya, biyowa bayan yakin basasa a Laberiya, wanda ya tilasa musu yin kaura.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China