in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane da dama sun rasu a harin da Boko Haram ta kai makarantu a arewacin Najeriya
2013-03-19 10:36:39 cri

Wata sanarwa da hukumar sojan Najeriya ta bayar na nuna cewar, kungiyar Boko Haram ta kai hari a makarantu guda uku ranar Litinin a garin Maiduguri dake arewacin Najeriya, inda mutane hudu suka rasu, sannan wasu guda uku suka samu rauni.

An kashe malami guda daya, kana dalibai guda uku sun samu mummunan rauni sakamkon harbin bindiga.

Cikin sanarwar da ya bayar, mai magana da yawun hukumar tsaro ta hadin gwiwa JTF, Col Sagir Musa ya bayyana cewa, jami'an tsaro sun kashe uku daga cikin masu kai harin yayin farmaki da suka kai a wata makarantar.

Sanarwar ta ci gaba da bayyana cewa, labari da hukumar tsaron ta samu ya nuna cewa, 'yan kungiyar Boko Haram sun kashe wani malami a makarantar sakandaren Sanda Karami, dake layin Ruwan Zafi, a unguwar Custom, cikin garin Maiduguri, kana an harbi wani mai suna Malam Kachalla ranar Litinin tsakanin karfe takwas zuwa tara na safe a cikin harabar makarantar.

Sanarwa ta kara da cewa, dalibai guda uku mata sun samu mummunan raunin harbin bindiga, inda jami'an JTf dake sintiri suka kai su asibitin koyarwar jami'ar Maiduguri, wato bayan sun iso wajen ke nan sakamakon kai komo na mutane da suka lura da shi a unguwar ta Custom.

Sanarwar ta soji ta ci gaba da cewa, dakarun soji sun cimma nasarar kawar da wani hari da 'yan kungiyar ta Boko Haram suka so su gudanar a wata makarantar sakandare dake unguwar Mafoni da Galadima, inda aka kashe 'yan ta'addan guda uku aka kuma kwato bindigogi kirar AK47 guda biyu, harsasai guda 200, rakoda na bidiyo guda biyu, na'urar comfuta guda daya da kuma babur mai kafa uku guda daya.

Sanarwar ta ce, ana kokarin kamo masu hannu a lamarin don a hukunta su.

Ko da yake mazauna unguwar sun ce, aka kashe malamai guda hudu a harin.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China