Dakarun kasar Somalia, tare da hadin guiwar dakarun kawo zaman lafiya na kungiyar hada kan kasashen Afirka, AU, suna kara kutsawa da kuma kwace yankunan da 'yan tawayen Al-shabaab ke iko kansu, a kudancin kasar dake kusurwar Afirka.
A cikin wannan mako ne dakarun na hadin gwiwa, suka kara samun kafuwa a garin Wanla Weyn, dake da nisan kilomita 93 daga Mogadishu, babban birnin kasar ta Somalia, har ma da wani tsohuwar cibiyar sojin saman Somalia dake da nisan kilomita 15 daga garin Wanla Weyn.
Sabbin wuraren da aka kwato suna da muhimmanci domin sune ke hade birnin Mogadishu da garin Baidoa, dake yankin kudancin kasar, wanda shi ma yanzu haka yana karkashin ikon dakarun AU da na gwamnatin kasar Somalia.
Wanla Weyn yana kan iyaka da ta hade yankunan Shabelle guda 2, da garin Baidoa dake kudancin kasar, da kuma Beletweyne dake arewacin Somalia.
Jami'ai sun ce, kwato wadannan cibiyoyi a Wanla Weyn zai hade Mogadishu da Baidoa.
Ministan tsaro na Somalia, Hussein Arab Isse na daga cikin jami'an da suka ziyarci cibiyar sojin da aka kwato kusa da Wanla Weyn. Ministan ya ce, kwato wannan gari babbar nasara ce ga Somalia inda ya yi kira ga mayakan Al-shabaab su hade da dakarun gwamnati.(Lami)