Kwamitin tsaro na MDD ya amince da kudurin kara tsawon lokacin aikin da kungiyar hada kan kasashen Afirka ke yi a kasar Somalia da ake yi wa lakabi da AMISOM na shekara daya, wato zuwa 28 ga watan Fabrairun shekara ta 2014.
Kwamitin tsaron mai mambobi 15 a cikin kudurin nasa ya yaba irin nasara da hukumar AMISOM ta cimma na rage yawan salwantar rayuwar fararen hula yayin aikin, tare kuma da yin kira ga AMISOM da ta kara jan damara a kan hakan.
Kudurin har wa yau ya amince da dauke takunkumi da aka kakabawa kasar Somalia na makamai tun shekarar 1992 a yunkuri da ake na kara inganta karfin dakaru dake yakar 'yan tawayen kungiyar Al-Shabaab.
Kundin na mai bayyana cewa, a cikin watanni 12, takunkumin ba zai shafi kawo makamai ko kayan aikin soja ba, da kuma samar da shawarwari da horo wanda aka tanada don kara ingantawa da gina dakarun gwamnatin tarayyar Somalia da kuma samar da tsaro ga jama'ar kasar.
To amma kundin na mai nuni cewa, dauke takunkumin bai shafi batun manyan makamai ba kamar na kakkabo jiragen sama, nakiya da dai makamantansu.(Lami)