in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Somalia na maraba da soke shawarar hana jigilar da makamai a kasar
2013-03-08 10:30:48 cri
Ran 7 ga wata, gwamnatin kasar Somalia ta nuna farin cikinta game da matakin soke shawarar hana jigilar da makamai na 'dan lokaci a kasar da kwamitin sulhu na MDD ya dauka.

Ran 6 ga wata, kwamitin sulhu na MDD ya tsai da kuduri cewa, zai soke shawarar hana jigilar da makamai na tsawon shekara guda da ya dorawa kasar Somalia, wanda ya kawo dakatar da matakin da aka dauka shekaru 20 da suka gabata.

Amma wannan kuduri bai kunshi dukkan makamai ba, wato kamar bindiga mai luguden wuta, harsashi mai linzami da dai sauran makamai masu nauyi, kananan makamai kawai ne abin ya shafa.

Ran 7 ga wata, shugaban kasar Hassan Sheikh Mohamud ya nuna yabo ga kudurin, tare da matukar nuna godiya ga kwamitin sulhu na MDD don fahimta da girmamawa da ya nuna wa kasar Somalia.

Firaministan kasar Abdi Said ya bayyana cewa, lamarin zai taimaka wa sojojin tsaron kasar wajen inganta karfinsu, tare kuma da taimakawa gwamnatin kasar da ta cimma kiyaye yanayi mai karko a kasar.(Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China