Wasu rahotannin baya bayan nan sun bayyana cewa, mayakan kungiyar 'yan kaifin kishin Islama ta Al-Shabaab dake kasar Somalia, sun sake kwace garin Hudur dake kudancin kasar, biyowa bayan janyewar da tawagar sojin hadin gwiwar kasar da Habasha suka yi daga yankin. Mazauna yankin na Hudur sun shaida wa manema labaru cewa, mayakan na Al-shabaab sun maye gurbin sojojin hadin gwiwar ne ba tare da wani musayar wuta ba.
Garin na Hudur, wanda shi ne babban birnin lardin Bakool, ya kasance karkashin ikon rundunar hadin gwiwar kasashen Habasha da Somalia har tsahon shekaru biyu, tun bayan da sojin Habasha suka ketara iyaka zuwa Somalia, domin fatattakar 'yan tawayen dake addabar yankin.
Sai dai janyewar wannan runduna a yanzu, ya baiwa dakarun na Al-Shabaab damar sake damke madafan ikon birnin.(Saminu)