Wakilin musamman na shugaban kungiyar da AU ta tura wa kasar Somalia da ake kira AMISOM, Boubacar Diarra, ya yi suka kan kisan gilla da a kai wa sabon zababben 'dan majalisar kasar, Mustafa Mohamed Mo'alin a birnin Mogadishu.
An kashe Mo'alin ne a Waaberi dake birnin Mogadishu a Somalia, yayin da yake kan hanyar dawowa daga salla ran Asabar da yamma.
Diarra ya bayyana cewar, 'yan majalisu su ne ke wakiltar mutanen Somalia don haka duk wani hari da aka kai wa 'yan majalisa, hari ne kan jama'ar kasa kuma ba za'a amince da hakan ba. Ya yi kakkausar suka kan harin da aka kaiwa 'dan majalisar kasar Somalia,wanda aka zaba makonni biyu da suka gabata,inda ya bayyana zaben a matsayin ci gaba da ake samu kan yanayin siyasa a kasar.
Ya ci gaba da cewa, kungiyar ta AMISOM za ta ci gaba da yin bakin kokarinta wajen taimakawa dakarun tsaron Somalia don a samu raguwar barazanar hare-hare a birnin na Mogadishu.
Ya ce, bisa la'akari da irin nasara da aka cimma na kawo karshen mulkin wucin gadi, Somalia da su kansu mutanen kasar sun rungumi sabuwar alkiblar siyasa, don haka, ba za'a bar hari irin wannan da ya gurguntar da gaggarumar nasara da aka cimma ba.(Lami)