Kungiyar Hezbul-Islam dake kasar Somalia ta bayyana ficewa daga kawance dake tsakaninta da Al-Shabaab, bayan shafe kimanin shekaru biyu da kulla wancan kawance. Cikin wata sanarwar da kakakin kungiyar ta Hezbul-Islam Mohamed Moalim ya rabawa manema labaru ranar Litinin din nan, kungiyar ta bayyana sabanin ra'ayi, a matsayin dalilinta na ficewa daga wancan kawance. Dangane da alakarta da sabuwar gwamnatin kasar kuwa, Mohamed Moalim, ya ce, Hezbul-Islam na maraba da dukkanin tattaunawa mai amfani, amma za su ci gaba da adawa da jibge sojojin kasashen waje a kasar.
Dama dai tun a baya shugaban kungiyar ta Hezbul-Islam Hassan Dahir Aweys, ke nuna rashin goyon baya ga cigaba da dorewar alakar kungiyoyin biyu, dama batun kulla alaka tsakanin Al-Shabaab da babbar kungiyar 'yan tada kayar baya ta al-Qaida, a shekarar da ta wuce.
Haka zalika Hezbul-Islam ta sha nuna rashin goyon bayanta ga amfani da masu jihadi daga ketare domin yaki da gwamnatin kasar ta Somalia, dama batun jibge sojojin samar da zaman lafiya na kungiyar kasashen Afirka a kasar.
Wannan dai mataki da kungiyar Hezbul-Islam ta dauka na ballewa, wani babban koma baya ne ga kungiyar Al-Shabaab, wadda ke cigaba da shan matsin lamba daga sojojin kasar dake samun tallafin sojojin samar da zaman lafiya na AU, daidai lokacin da hadin gwiwar sojojin ke kokarin kwace tashar ruwan Kismayo dake kudancin kasar, cikin muhimman wurare da a yanzu ke karkashin ikon kungiyar ta Al-Shabaab.(Saminu)