Faraministan kasar Masar Kamal El-Ganzouri ya bayyanawa 'yan jarida cewa, gwamnatinsa ta dauki niyyar kebe Livres kudin kasar miliyan 150 kimanin dalar Amurka miliyan 25 domin gidajen jama'a 76,000 ga mutanen kasar dake da karancin kudin shiga.
Kusan kimanin iyalai miliyan 1,26 zasu ci gajiyar wannan pansho a cikin kasar baki daya.
Haka gwamnatin kasar Masar ta dauki niyyar shigar da Livres miliyan 200 kudin Masar kwatankwacin dalar Amurka miliyan 33 zuwa kananan masana'antu bisa burin samar da ayyukan yi ga jama'a, in ji malam Ganzouri tare da kara bayyana cewa, gwamnatin kasar zata cigaba da dukufa wajen amincewa da tsarin dokar sake duba dokokin dake da nasaba da zuba jari. (Maman Ada)