A cikin rahotonta, kasar Sin ta ce, gwamnatin Amurka, wadda ta kan mayar da kanta tamkar mai yaki da keta hakkin dan Adam, ta gabatar da rahoto a kwanan baya kan halin da kasashen duniya suke ciki a fannin kare hakkin dan Adam a shekarar 2012, inda ta sake tsoma baki kan harkokin hakkin dan Adam na kasashe fiye da 190, ciki har da kasar Sin, amma ba ta ce kome ba kan halin da ita kanta ke ciki.
Hakikanin al'amura na zahiri sun nuna cewa, Amurka na fuskantar munanan matsaloli a fannin kiyaye hakkin dan Adam, lamarin da ya jawo soke-soke daga kasashen duniya.
A cikin rahotonta kan halin da Amurka take ciki ta fuskar hakkin dan Adam a shekarar 2012, kasar Sin ta tono yadda Amurka ta keta hakkin dan Adam a fannoni guda 6, wadanda suka hada da fagen kare rayukan mutane da tsaron lafiya, hakkin al'ummar kasa da hakkinsu ta fuskar siyasa, tattalin arziki da zamantakewar al'ummar kasa, wariyar al'umma, hakkin mata da yara, da keta hakkin dan Adam a sauran kasashe.
Wannan ne karo na 14 a jere da kasar Sin ta kaddamar da irin wannan rahoto domin mayar da martani ga rahoton shekara-shekara da Amurka ke gabatarwa kan harkokin hakkin dan Adam na kasa da kasa.(Tasallah)