Sabon shiri game da kare hakkin dan Adam na nuna kokarin kasar Sin na kara azama ga kare hakkin dan Adam
A ranar 11 ga wata, ofishin kula da harkokin yada labaru na majalisar gudanarwa ta Sin ya fitar da shirin kare hakkin dan Adam daga shekarar 2012 zuwa shekarar 2015, abin da ya jawo hankalin jama'a a gida da waje. Direktan ofishin kula da harkokin yada labaru na majalisar gudanarwa ta Sin Wang Chen a zantawarsa da wakilinmu, inda ya bayyana cewa, a cikin sabon shirin kare hakkin dan Adam da aka fitar, an nuna kokarin gwamnatin Sin na nacewa ga sa kaimi wajen kare hakkin dan Adam na kasar, kuma hakan ya nuna cewa, kare hakkin dan Adam ya shiga wani sabon mataki yadda ya kamata.
Wang Chen ya ce, idan aka kwatanta shirin farko da sabon shirin da aka gabatar a wannan lokaci, za a fahimci cewa, sabon shirin na nuna matsayin da kasar Sin ke tsayawa wajen kare hakkin dan Adam, kuma an tsara shirin ne bisa shirin samun bunkasuwa karo na 12 na shekaru biyar-biyar.
Ya yi bayanin cewa, ana ci gaba da kare hakkin dan Adam daga dukkan fannoni, tare da jaddada rawar da kungiyoyi da kafofin yada labaru ke takawa wajen kare hakkin dan Adam, don haka, ya kuma bukaci al'umma da su yada sha'anin kare hakkin dan Adam, da fadakar da jama'a game da matakan kare hakkin dan Adam, da daukaka ingancin ra'ayoyinsu a wannan fanni.(Bako)