An yi tambayar cewa, a ran 24 ga wata, majalisar harkokin wajen kasar Amurka ta kaddamar da rahoto kan kiyaye hakkokin dan Adam na kasa da kasa na shekarar 2011, inda ta sake yin zargi kan yanayin da kasar Sin take ciki ta fuskar kare hakkokin dan Adam. Mene ne ra'ayin kasar Sin kan lamarin?
Hong Lei ya bayyana cewa, a cikin shekaru 30 ko fiye bayan da kasar Sin ta fara yin gyare-gyare a gida tare da bude kofarta ga kasashen waje, ta samu manyan ci gaba wajen kiyaye hakkokin dan Adam. Wannan shi ne hakikanin abun da kowa ya iya gani. Amurka ta kan yi sharhi kan harkokin cikin gida na sauran kasashe a cikin rahotonta. Ta tabo maganar hakkokin dan Adam na kasar Sin ne da tunaninta kawai ba bisa hakikanin abubuwa ba. Rahoton ya mayar da baki fari. Ba ya isa a yi muhawara da shi.
Mista Hong ya kara da cewa, ana bukatar rika kyautata ayyukan kiyaye hakkokin dan Adam. Kasashen duniya na iya yin tattaunawa da juna cikin adalci a game da kiyaye hakkokin dan Adam, a kokarin kara fahimtar juna da sa kaimi tare da juna. Amma bai kamata ba a tsoma baki cikin harkokin cikin gida na sauran kasashe bisa hujjar kare hakkokin dan Adam. Kasar Sin ta shawo kan Amurka da ta dubi halin da ita kanta take ciki a tsanake, ta dakatar da tunani da daukar matakan da ba daidai ba ta fuskar kiyaye hakkokin dan Adam. (Tasallah)