A ranar Alhamis ne kasar Sin ta yi kira ga kasashen duniya da su tabbatar da inganta adalci, aminci, shigar da jama'a da kuma cimma nasarar hadin gwiwa a fuskar kare hakkin bil adama tsakanin kasa da kasa.
Liu Zhenmin wanda shi ne wakilin kasar Sin a ofishin kare hakkin bil adama na MDD da ma wasu kungiyoyin kasa da kasa dake birnin Geneva a kasar Switzerland ya yi jawabi yayin zaman muhawara jiko na 22 na majalisar kare hakkin bil adama, inda ya ce, ana fuskantar kalubale da dama a fuskar kare hakkin bil adama a duniya.
Liu ya ci gaba da cewa, yayin babban taronta na kasa jiko na 18, jami'yyar kwaminis ta kasar Sin ta dora fiffiko kan matsayin jama'a ganin cewa, su ne jigo na kasar, tare kuma da yin kiran a kare hakkinsu da ma bullo da sabbin matakai don moriyarsu.
Kasar Sin ta mika bukatarta na takarar zama mamba a hukumar kare hakkin bil adama a shekarun 2014 zuwa 2016, in ji Mr. Liu, inda hakan ke nuna cewa, kasar Sin ta sha damarar aiki tare da sauran al'ummar duniya da kuma ba da gudummawar samun ci gaba wanda ya dace, a fuskar kare hakkin bil adama.(Lami)