in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta fitar da shirinta na kiyaye hakkin dan Adam na shekarar 2012 zuwa shekarar 2015
2012-06-11 16:34:47 cri
Bayan da majalisar gudanarwa ta Sin ta bayar da izni, a ranar 11 ga watan Yuni, ofishin kula da harkokin yada labaru na majalisar gudanarwa ta kasar ta fitar da wani tsari game da kiyaye hakkin dan Adam daga shekarar 2012 zuwa shekarar 2015, kuma wannan wani shirin raya kasa ne da ya shafi hakkin dan Adam na biyu da gwamnatin Sin ta fitar. Haka kuma, domin ci gaba da kiyaye hakkin dan Adam na kasar, wannan shiri ya bayyana burin da Sin ta bayyana gaba game da ci gaba da kiyaye hakkin dan Adam cikin shekaru 4 masu zuwa.

Haka kuma, shirin ya ci gaba da bayar da muhimma kan kiyaye hakkin zaman rayuwar jama'a da samun bunkasuwa, domin ci gaba da kiyaye da kyautata zaman rayuwar jama'a, da kara himma wajen warware batutuwan da suka shafi moriyar jama'a, da inganta tattalin arziki da zamantakewar al'umma da al'adu, da kokartawa wajen samu ci gaban domin moriyar jama'a.

Bugu da kari kuma, tsara wani sabon shirin yana da ma'ana ta musamman wajen samun ci gaban kimiyya da kara azama ga kafa zamantakewar al'umma mai adalci da jituwa, da kokarta wajen kawo kwarin gwiwa da alheri ga ko wane mutum, ta hakan, jama'a za su iya samu zaman wadata.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China