Rahoton da kasar Sin ta kaddamar ya nuna cewa, rahoton da Amurka ta kaddamar kan hakkokin dan Adam a kasashen duniya ya sake yin sharhi kan yadda kasashe da yankuna kusan dari 2 na duniya suke kiyaye hakkokin dan Adam, tare da yin karin gishiri da yin zargi kan hakkokin dan Adam a kasar Sin. Amma bai ce kome ba kan tabarbarewar yanayin da Amurka take ciki wajen kiyaye hakkokin dan Adam.
Rahoton ya kara da cewa, kamata ya yi Amurka ta fuskanci manyan matsalolin da take fuskanta a fannin kiyaye hakkokin dan Adam yadda ya kamata, ta daina sanya siyasa cikin batun kiyaye hakkokin dan Adam domin shafa wa sauran kasashe kashin kaji, tsoma baki cikin harkokin cikin gida na saura, da neman samun moriya bisa manyan tsare-tasre, kana kuma ta dakatar da aiwatar da ma'aunai guda 2 ta fuskar kare hakkokin dan Adam da nuna isa bisa hujjar kare hakkokin dan Adam.(Tasallah)