in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ba za'a iyar tunbuke faraministan Afrika ta Tsakiya ba a tsawon lokacin rikon kwarya, in ji ECCAS
2013-04-19 11:00:05 cri

Shugabannin kungiyar kasashen dake tsakiyar Afrika (ECCAS) da suka halarci wani zaman taro na musammun na ranar Alhamis a birnin N'Djamena na kasar Chadi, sun amince da cewa, faraministan kasar Afrika ta Tsakiya na da cikakken iko kuma shugaban kasar ba zai iyar sallamarsa ba a tsawon lokacin rikon kwaya na watanni 18.

Wannan zaman taro karo na hudu na kungiyar ECCAS ya fitar da wata sanarwa tare da jadawalin aiki dake da nasaba yawan mambobin da za su kunshi kwamitin rikon kwarya na kasa CNT da kuma yadda zai aiki. A cewar sanarwar N'Djamena, faraministan kasar Afrika ta Tsakiya, Nicolas Tiangaye da tsohon shugaban kasar Francois Bozize ya nada a cikin watan Janairu bisa yarjejeniyar Libreville da aka rattabawa hannu a ranar 11 ga watan Janairu na da cikakken iko. Kuma shugaban kasa ba zai iyar sallamarsa ba a duk tsawon lokacin rikon kwarya, haka kuma yana da nauyin kafa sabuwar gwamnatin rikon kwarya ta hanyar yin shawarwari tare da bangarori daban daban na kasar Afrika ta Tsakiya bisa tushen yarjejeniyar Libreville, in ji wannan sanarwa.

A wata sabuwa kuma, yau 19 ga wata, Madam Hua Chunying, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayyana cewa, kasar Sin ta nuna yabo ga kungiyar ECCAS da kokarinta wajen neman warware matsalar kasar Afirka ta tsakiya.(Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China