in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Magatakardan MDD ya damu matuka dangane da tabarbarewar tsaro a Afirka ta tsakiya
2013-04-17 10:28:45 cri

A ranar Talata, babban sakataren MDD Ban Ki-Moon ya bayyana cewa, ya damu matuka dangane da yanayin tsaro dake tabarbarewa a CAR, jamhuriyar Afirka ta tsakiya, inda a kalla mutane 20 suka rasa rayukansu sakamakon fadace-fadace, inda kuma ya yi suka mai karfi kan aikace-aiakacen kungiyar 'yan tawayen Seleka dangane da tada hankalin jama'a fararen hula.

Wata sanarwa da mai magana da yawun magatakardan MDD Martin Nesirky ya bayar, na mai nunin cewa, magatakardan MDD na kira ga shugabanin da su maido da doka da oda a fadin kasashensu, kuma tabbatar da kare fararen hula.

Rahotanni na nuna cewa, a kalla mutane 20 sun rasa rayukansu a karshen makon da ya wuce sakamakon fadace-fadace tsakanin 'yan tawayen gammayar Seleka da dakaru dake goyon bayan shugaban kasar da a kai wa juyin mulki, Francoise Bozize.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, magatakardan na MDD ya jadadda cewa, wajibi ne masu aikata laifuffuka su amsa laifinsu.

A halin da ake ciki, sanarwar ta kara da cewa, sakatare janar din ya jadadda cewa, wajibi a yi amfani da yarjejeniyar Lebreville ta zamo matashiyar kowane irin mataki na siyasa da za'a dauka don warware rikicin a kasar.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China