Kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin ya yi jawabi game da halin da ake ciki a Afirka ta Tsakiya
Dangane da tsanantar halin da ake ciki a kasar Afirka ta Tsakiya da kuma mutuwa da raunatar sojojin kasar Afirka ta Kudu dake kasar, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Qin Gang ya bayyana a ranar 26 ga wata cewa, kasar Sin ta jajantawa iyalan sojojin kasar Afirka ta Kudu da suka mutu da kuma wadanda suka ji rauni a yakin da ya faru a kasar Afirka ta Tsakiya, yana mai cewa, Sin tana lura sosai kan halin siyasa da tsaron kasar Afirka ta Tsakiya. Kuma ba ta amince da kwace mulki ta hanyar karfin soja ba, don haka sai ta yi kira da a warware rikicin kasar ta hanyar siyasa da kuma maido da zaman lafiya cikin hanzari. Ban da wannan kuma, a cewarsa kasar Sin tana nuna goyon baya ga kasar Afirka ta Kudu da kungiyar AU da sauran hukumomin kasa da kasa da su kara kokari wajen warware matsalar, kuma har ila yau Sin tana son taimaka musu in bukatan hakan ya tashi. (Zainab)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku