Sakatare janar na MDD Ban Ki-moon ya yi allawadai a ranar Lahadi da juyin mulkin 'yan tawayen Seleka a kasar Afrika ta Tsakiya tare da yin kira da a maido tsarin mulkin kasar cikin gaggawa.
Ban Ki-moon na mai Allah wa dai da wannan juyin mulki dake sabawa kundin tsarin mulki da ya faru a kasar Afrika ta Tsakiya a ranar 24 ga watan Maris na shekarar 2013, tare kuma da yin kira da maido tsarin mulkin cikin gaggawa, in ji wata sanarwar da aka fitar a ranar lahadi.
'Yan tawayen Seleka sun kwace Bangui, babban birnin kasar bayan da shugaban kasar Francois Bozize ya arce daga fadarsa, a cewar wasu rahotonni a ranar Lahadi.
Karbe birnin Bangui ya kasance babban mataki har zuwa wannan lokaci na 'yan tawaye da ake kira Seleka dake nufin kawance a cikin harshen Sango.
Haka kuma sanarwar ta sakatare janar na MDD ta jaddada cewa, yarjejeniyoyin Libreville, da shugabanni da gwamnatocin kungiyar kasashen CEEAC suka cimma su ne kadai hanya mafi kyau wajen tabbatar da zaman lafiya mai karko a cikin wannan kasa. (Maman Ada)