An bayyana matukar bukatar da ake da ita, ta dowa da kyakkyawan yanayin zaman lafiya, da bin doka da oda a jamhuriyar Afirka ta tsakiya, tare da kaucewa keta hakkin bil'adama da barnata dukiyoyi a kasar.
Wata sanarwa da kwamishiniya mai lura da harkokin da suka shafi kare hakkin bil'adama ta MDD Navi Pillay ta fitar a ranar Talata 16 ga wata, ta bayyana cewa, an kashe sama da mutane 20 a birnin Bangui cikin karshen makon da ya gabata kadai, bayan da aka yi kiyasin kisan a kalla mutane 119, tun lokacin da 'yan tawayen Seleka suka karbe mulkin kasar a ranar 24 ga watan Maris da ya gabata.
Ana dai zargin bangarori daban daban da aikata laifukan wawashe dukiyoyin jama'a, da kuma lalata kayayyakin more rayuwar jama'a daban daban.
Bugu da kari, Pillay ta jaddada cewa, keta harkokin bil'adama, ba abu ne da za a amince da aukuwarsa ba, don haka ya zama wajibi a dauki matakan duk da suka dace, domin tabbatar da doka da oda, tare da hukunta dukkanin wadanda aka kama da laifin karya doka. Daga nan sai ta yi kira da majalissar rikon kwaryar kasar, da ta gaggauta karfafa ikon doka, da kare hakkin fararen hula.(Saminu)