Rundunar 'yan tawayen Seleka wacce ta hambarar da gwamnatin jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ta ce, sai nan da shekaru 3 masu zuwa ne za a gudanar da babban zabe a kasar.
Wata kafar watsa labarai ta kasar Faransa ta rawaito mai magana da yawun kungiyar na cewa, Seleka na ci gaba da kokarin dawo da yanayin zaman lafiya a babban birnin kasar Bangui, bayan juyin mulkin da ya auku a ranar Lahadin da ta gabata. Haka zalika, kafar watsa labarun ta ce, bata gari sun yi amfani da hatsaniya da zaman dar dar da juyin mulkin ya haifar, wajen wawashe dukiyoyin al'umma, lamarin da kungiyar Seleka ke cewa, za ta tabbatar da magance shi.
Kungiyar ta ce, karar harbe-harbe da aka rika ji a ranar Litinin 25 ga wata ba wani abun damuwa ba ne, illa dai magoya bayan rundunar ne ke nuna farin cikinsu da nasarar da suka samu, kamar dai yadda kakakin kungiyar
na nahiyar Turai Eric Massi ya tabbatar da hakan. Massi ya kuma kara da cewa, Seleka za ta ci gaba da martaba yarjejeniyar da aka cimma a baya, wadda ta bai wa Nicolas Tiangaye damar kasancewa firaministan gwamnatin hadakar kasar, har ya zuwa karshen lokacin rikon kwarya.
A baya dai kungiyar ta Seleka ta rattaba hannu kan yarjejeniyar tsagaita wuta da tsagin gwamnati a birnin Libreville na kasar Gabon, kafin daga bisani ta sake sauya matsayarta, bisa zargin da ta yi wa shugaba Bozize, na kin martaba sharuddan da aka cimma, tare da yin watsi da baiwa tsohon shugaban damar karshen zangon mulkinsa zuwa shekara ta 2016.(Saminu)