Kwamitin tsaron MDD ya yi matukar Allah wadai, da kisan wasu dakarun wanzar da zaman lafiya su 5, da fararen hula kimanin 7 a kasar Sudan ta Kudu, yana mai kira ga gwamnatin kasar, da ta tabbatar da hukunta wadanda suka aikata wannan mummunan laifi.
Wannan dai sako na kunshe ne cikin wata sanarwa, da shugaban kwamitin na watan Afirilun nan, kuma manzon kasar Ruwanda a majalissar Eugene Richard Gasana ya karanta wa manema labaru a ranar Talata 9 ga wata.
Sanarwar ta kara da bayyana alhinin mambobin majalissar, tare da mika sakon ta'aziyya ga iyalan dakarun kasar India 5, da ragowar fararen hular da wannan hari ya ritsa da su, tana kira ga dukkanin masu ruwa da tsaki a kasar, da su hada kai da rundunonin wanzar da zaman lafiya, domin cimma burin da aka sanya gaba.
Wannan dai sanarwa ta biyo bayan sakon babban magatakardar MDD Ban Ki-Moon, wanda shi ma ya yi tir da kisan wadancan jami'ai, tare da yin kira da a hukunta wadanda suka aikata hakan.
Rahotanni dai sun tabbatar da cewa, wasu 'yan tawaye dauke da makamai ne suka bude wuta kan tawagar MDD, dake kunshe da sojojin kasar India 32, ranar Talata 9 ga wata, a yankin Jonglei, dake kudancin kasar ta Sudan ta Kudu, yankin da tuni mahukuntan kasar suka bayyana shi a matsayin yanki mai matukar hadari. A halin da ake ciki, akwai dakarun MDD kimanin 1,000 a yankin.(Saminu)