in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jam'iyyun siyasa a Zimbabwe sun gudanar da yakin neman zabe mai zafi gabanin kuri'ar raba gardamar kasar
2013-03-15 10:39:32 cri

Manyan jam'iyyun siyasar kasar Zimbabwe biyu sun kaddamar da yakin neman zabe mai zafi na babban zaben kasar dake tafe, yayin da suke goyon bayan daftarin kundin tsarin mulkin kasar da al'ummar kasar za su kada kuri'ar raba gardama kansa a ranar Asabar.

Yayin da shugaban kasar Robert Mugabe na jam'iyyar Zanu-PF da Firaministan kasar Morgan Tsvangirai na jam'iyyar MDC-T ke kamfel din ganin an kada kuri'ar raba gardamar, su kuma jam'iyyun suna gabatar da manufofinsu na zabe ga jama'a, inda dukkan 'yan takarar ke bayyana cancantarsu na mukaman da suke nema a zabe a daftarin kundin tsarin mulkin tare da cewa, za su cika alkawuransu na inganta rayuwar jama'a, ta hanyar bullo da manufofin da za su dace da tsarin mulkin kasar.

Dukkan 'yan takarar sun yi kokarin karade sassan kasar don tallata manufofinsu ga masu kada kuri'a da kuma bayyana tasiri ko rashin tasirin kada kuri'ar raba gardamar da ke tafe.

Jam'iyyar MDC-T da Zanu-PF sun gabatar da dalilai da dama na goyon bayan daftarin tsarin mulkin kasar, kamar samar da aikin yi, mallakar takardar izinin zama 'dan kasa guda biyu, kirkiro hukumar hukunta masu aikata laifuffuka ta kasa, wa'adin shugaban kasa da manyan jami'an gwamnati a kan mulki,wakilcin kashi 50 cikin 100 na mata a mukamai da dai sauransu.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China