A ranar Alhamis din nan ne shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan ya kawar da dukkan wani zato na yafewa 'yan kungiyar Boko Haram muddin suka ci gaba da boye kansu.
Yayin da yake amsa tambayoyi daga dattijai yayin wani taron jama'a a Damaturu, shugaba Jonathan ya ce, gwamnati ba za ta yafe 'yan kungiyar ba har sai sun gabatar da kansu.
Shugaban ya ce, ba za'a iya yafewa mutane dake boye ba, tare da karin cewa, ya kamata su gabatar da kansu ga gwamnati kafin a yi tunanin yafe musu.
Shugaban na Najeriya ya kuma musanta zargin da ake mai cewa, ziyayar tasa makararriya ce a jihar da take fama da 'yan tawaye. Ya ce, ba gaskiya ba, cewar shugaban kasa, bai damu da jihohin Borno da Yobe ba saboda kalubale na tsaro, inda ya ci gaba da cewa, da ya zo jihar Yobe tun lokutan baya domin dukkan abin da ya shafi wani bangaren kasar ya shafi kasar baki daya.
Shugaban na Najeriya ya ci gaba da cewa, ta'addanci abu ne da ya shafi duniya baki daya domin ba mutanen yankin ne kadai abin ke shafa ba, kuma wannan lamari bai shafi siyasa ba.
Ya ce, gwamnatin tarayya za ta hada kai da jihohin da abin ya shafa don ba da tallafi ga wadanda abin ya shafa, kamar mata da marayu.
Shugaba Jonathan ya kuma ba da tabbacin cewa, gwamnati za ta aiwatar da shirin kawar da talauci ta hanyar samar da aikin yi ga jama'a.(Lami)