in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nijar ta karyata labaran dake nuna cewa sojojinta sun jikkata a Mali
2013-03-01 10:14:48 cri

Ministan tsaron kasar Nijar Mahamadou Karidjo ya karyata wasu labarai a ranar Alhamis dake nuna cewa, an iso a birnin Yamai da sojojin kasar da suka jikkata a kasar Mali.

Jaridar 'I'Evenement' mai zaman kanta, ta ruwaito da wannan labari a cikin fitowarta ta ranar 23 ga watan Febrairun da ta gabata dake nuna cewa, sojojin Nijar fiye da goma sun samu raunuka a cikin wani kazamin fadan baya baya a kasar Mali.

A cikin sanarwarsa, mista Karidjo ya nuna cewa, wannan labari ba ya da sahihancin gaskiya. Haka kuma ya kara da cewa, har zuwa wannan rana babu wani sojin nijar da ya mutu ko ya ji rauni a cikin tawagar rundunar sojojin kasar da aka tura kasar Mali dake imani da nauyin kare aikinsu bisa goyon bayan 'yan nijar da gamayyar kasa da kasa, in ji wannan sanarwa. Tare da jaddada yabo da jinjinawa ga sojojin da aka tura a cikin ayyukan dake gudana a kasar Mali, minista Karidjo ya dauki niyyar rika sanar da al'ummar Nijar ko da yaushe kan halin da ake ciki a kasar Mali.

Kasar Nijar ta tura sojoji 680 zuwa arewacin kasar Mali domin fatattakar kungiyoyin 'yan ta'adda a cikin tawagar rundanar sojojin kiyaye zaman lafiya a kasar Mali wato MISMA. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China