in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Cyprus ya yi kira ga jama'a da su yi hadin gwiwa domin farfado da tattalin arzikin kasa
2013-03-26 16:12:22 cri
A daren ranar 25 ga wata, shugaban kasar Cyprus Anastasiades ya ba da jawabi ta kafar telibiji, inda ya yi kira ga jama'ar kasar da su kwantar da hankalinsu, tare da yin hadin kai da gwamnatin kasar a kokarinta na farfado da tattalin arzikin kasar cikin gajeren lokaci, bisa imani da kokarin da ake yi.

Haka nan ya kara da cewa, an yi fama da mawuyacin hali, na cimma wannan yarjejeniyar ba da ceto, ko da yake wannan ce yarjejeniya mafi kyau da aka iya cimmawa a halin yanzu. Ban da haka, ya yi watsi da shawarwarin wasu sassa, dake bukatar daukar matsayin janyewa daga rukunin kasashe masu amfani da kudin Euro, ko kuma batun neman wata hanya ta daban, ba tare da neman taimakon tarrayar EU.

Da safiyar yau Talata 26 ga wata ne, babban bankin Cyprus ya sanar da ci gaba da rufe kofofin dukkanin bankunan kasar, har tsawon kwanaki biyu masu zuwa, wato zuwa ranar 28 ga watan nan kafin sake bude bankunan.

An ba da labarin cewa, sakamakon matsayar da ministocin kudi na wasu kasashe dake rukunin kasashe masu amfani da kudin Euro suka cimma, na zartas da sabuwar yajejeniyar ba da tallafi ga kasar ta Cyprus, kungiyar EU, da IMF, da babban bankin nahiyar Turai sun cimma matsaya, don haka babban bakin nahiyar ta Turai ya sanar da cewa, zai samar da tallafi cikin gaggawa ga kasar Cyprus, domin hana dirkushewar tattalin arzikinta. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China