A ranar Laraba 13 ga wata, shugaban babban bankin jama'ar kasar Sin Zhou Xiaochuan ya ce, adadin CPI na kasar Sin a watan Fabrairu na shekarar bana ya kai kashi 3.2 bisa dari, wanda ya samar da adadin da aka yi tsammani a da, lamarin da ya bayyana wajibcin mai da hankali kan hauhawar farashin kayayyaki.
Zhou Xiaochuan ya yi wannan furuci ne yayin wani taron manema labaru da aka yi a wannan rana a cibiyar watsa labarai a taro na farko na majalisar wakilai na 12 na jama'ar kasar Sin.
Shugaban babban bankin jama'ar kasar sin ya yi bayanin cewa, bankin ya na sa ido kan ma'aunin CPI, kuma yana shirin ba da tabbaci ga farashin kayayyaki ta hanyar daukar manufar kudi da sauran matakai da suka dace da kuma hana hauhawar farashin kayayyaki ba bisa shiri ba. (Amina)