in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bukaci Sudan da Sudan ta kudu da su aiwatar da yarjejeniyarsu
2013-03-14 09:47:41 cri

Ministocin harkokin wajen kasashen Amurka, Norway da Birtaniya a jiya Laraba 13 ga wata suka bukaci kasashen Sudan da Sudan ta kudu da su fara aiwatar da yarjejeniyar da suka rattaba ma hannu daga dukkan fannoni nan take ba tare da wassu sharudda ba.

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry, da na Norway, Espen Barth Eide da kuma na Birtaniya William Hague wadanda ake ma lakabi da Sudan Troika, a sanarwar hadin gwiwa sun yaba da tsarin da kasashen biyu suka amince a ranar Jumma'ar da ta gabata, na ganin sun aiwatar da yarjejeniyoyi guda 9 da shugabannin biyu suka rattaba ma hannu a watan Satumbar bara ta 2012.

Kasashen biyu sun amince a ranar Talata da su maido da jigilar fitar da man fetur kasashen waje cikin yankin Sudan, sakamakon janye sojojinsu a kan iyaka a ranar Lahadin da ya gabata, tare da samar da wani yanayi da babu jami'an tsaron soji a wajen.

Da suke jinjina ma wannan sabon mataki, ministocin harkokin wajen kasashen uku sun kuma yi kira da a tabbatar da ganin an aiwatar da duk yarjejeniyar nan take ba tare da wani sharudda ba, kamar yadda MDD ta bukata a dokarta mai lambar 2046 da suka hada da matsayin garin Abyei mai arzikin man fetur.(Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China