Wata sanarwa da ta fito daga ofishin shugaban kasar Faransa Francois Hollande, ta bayyana cewa, shugaban na Faransa ya zanta da takwaransa na Afirka ta Kudu Jacob Zuma ta wayar tarho, don gane da halin da ake ciki a kasar Afirka ta Tsakiya.
Sanarwar ta ce, shuwagabannin biyu sun bukaci dukkanin bangarorin kasar da su kaucewa ta da hankula, da wawashe dukiyoyin al'umma, su kuma martaba yarjejeniyar da aka cimma a birnin Libreville. Wannan dai sanarwa na zuwa ne bayan da dakarun kungiyar Seleka suka kwace ikon babban birnin kasar Bangui a ranar Lahadi 24 ga wata.
Tuni dai shugaba Hollande ya tattauna da babban sakataren MDD Ban Ki-Moon, da shugaban kasar Chadi Idriss Deby Itno, wanda ya jagoranci kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen dake tsakiyar nahiyar Afirka, don gane da rikicin jamhuriyar Afirka ta Tsakiyar. Rahotannin baya-bayan nan sun tabbatar da tura sojin Faransa 350 zuwa jamhuriyar Afirka ta Tsakiyar a karshen makon jiya, domin tabbatar da ba da kariya ga 'yan Faransa dake kasar.(Saminu)