in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yan tawaye na ci gaba da rike ikon garuruwa 7 a kasar Afirka ta tsakiya
2013-03-05 14:25:20 cri

Kakakin rundunar 'yan tawayen jamhuriyar Afirka ta tsakiya Kanar Michel Narkoyo, ya bayyana cewa, har zuwa yanzu suke rike da garuruwan kasar 7, bayan janyewarsu daga yankin Damara, dake da nisan kilomita 90 daga arewacin birnin Bangui. Narkoyo ya kara da cewa, kungiyar tasu ce ke rike da ikon yankunan arewaci, da gabashi, da na tsakiyar kasar.

Rahotanni dai sun bayyana cewa, kungiyar ta Seleka na rike da mafi yawan yankunan kasar, in ban da birnin Bangui dake samun kariya daga rundunar kungiyar habaka tattalin arzikin kasashen tsakiyar nahiyar Afirka ta CEEAC.

Idan dai ba a manta ba, an kafa kungiyar 'yan tawayen ta Seleka ne cikin watan Disambar bara, da nufin hambarar da shugaba Francois Bozize daga mukaminsa, ta kuma sanya hannu kan yarjejeniyar sulhu da tsagin gwamnati, cikin watan Janairun da ya gabata a birnin Libreville na kasar Gabon. Kuma tun kafuwar gwamnatin hadin gwiwa karkashin jagorancin shugaban 'yan adawa Nicolas Tiangaye ran 3 ga watan Fabrairun da ya wuce, ake ta samun baraka a kungiyar, sakamakon aniyar kwance damarar yaki da ake da burin aiwatarwa ga kungiyar ta Seleka.

Kungiyar dai na ganin wannan mataki zai yi nasara ne kawai, idan sojojin kasashen Afirka ta Kudu, da na Uganda, dake goyon bayan shugaba Bozize, suka amince da ficewa daga kasar, aka kuma saki firsinonin siyasa da ake tsare da su.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China