in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a gina hanyar mota mai tsawon kilomita 450 a arewacin kasar Nijar
2013-01-11 14:03:06 cri

Kasar Turkiya ta dauki niyyar nan ba da dadewa wajen gina hanyar motar arewacin Nijar ko "boucle du l'Air" a jihar Adadez dake kuriyar arewacin kasar mai tazarar kilomita 450, a cewar faraministan kasar Turkiya mista Recep Tayyip Erdogan a kwanan nan a yayin wani taron manema labarai da ya cike karshen ziyarar aiki ta kwanaki biyu a kasar Nijar. Wannan hanya za ta hade Agadez, hedkwatar yankin Air da sauran manyan biranen jihar wadanda suka hada da Arlit, Iferouane, Elmeki da Timia, kuma za'a gina ta cikin 'dan gajeren lokaci mai zuwa, tare da taimakon kudin da za'a tattauna neman rancensu daga bankin Exim Bank, mallakar kasar Sin, in ji shugaban gwamnatin kasar Turkiya. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China