in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zimbabwe za ta kafa kotunan shari'a na musammun game da zabe domin yin rigakafin tashe-tashen hankalin siyasa
2012-11-02 10:31:56 cri

Hukumomin kasar Zimbabwe sun bayyana niyyar kafa wasu kotunan shari'a na musammun game da zabe domin daidaita matsalolin da ka iyar bullowa ta fuskar siyasa a lokacin zabubuka masu zuwa, in ji hukumar zabe ta kasar Zimbabwe (ZEC).

Mataimakiyar shugaban hukumar zabe, wato madam Joyce Kazembe ta shedawa kamfanin dillancin labarai na kasar Zimbabwe cewa, wadannan kotuna za'a kafa su ne domin daidaita tashe-tashen hankali da ka iyar abkuwa masu nasaba da siyasa a yayin zabubukan da za'a gudanar a farkon shekarar 2013.

Wannan wani kundin doka ne da ya shafi jam'iyyun siyasa, in ji madam Kazembe tare da bayyana hukuncin da zai biyo baya ga jam'iyyun siyasa na kasar idan sun take shi.

Hakazalika, madam Joyce Kazembe ta jaddada cewa, ZEC ta gudanar da tarurukan kara wa juna sani tare da jam'iyyun siyasa 23 a cikin kasar da nufin fadakar da su kan matakan zabe da dokar zabe, ta yadda za su iyar kaucewa take dokokin zabe.

Faraministan kasar Morgan Tsvangirai ya janye daga takarar shugaban kasa a shekarar 2008 tare zargin cewa, magoya bayansa sun sha azabar tashe-tashen hankalin siyasa.

Sai dai a baya bayan nan, shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe ya mai da hankali kan neman jituwar al'ummomin kasar Zimbabwe baki daya duk da bambancin ra'ayin siyasa da ake samu. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China