Yau Talata 16 ga wata, gwamnatin kasar Sin ta gabatar da takardar aikin tsaron kasa mai jigon "Hanyoyi daban-daban da dankarun kasar Sin ke bi ", inda karo na farko ne aka gabatar da hakikanin adadin sojin kasa, na sama da na ruwa, kuma hakan ya samar da karin haske a wannan fanni.
Wannan shi ne karo na takwas da gwamnatin kasar ta gabatar da irin wannan takarda tun daga shekarar 1998, kuma shi ne karo na farko da Sin ta gabatar da ita da sharhi. Wannan takarda ta bayyana manufofi da ka'idoji masu tushe da dankarun kasar Sin ke dauka, tare kuma da yin bayani kan hanyoyi daban-daban da suke bi, da yadda suke gudanar da ayyukansu.
Har ila yau a cikin takardar, a karo na farko an gabatar da adadin sojin kasa, lakabinsa da kuma adadin sojin ruwa da na sama. Ban da haka, karo na farko ne aka gabatar da nauyin dake wuyansu na kiyaye sararin teku da moriyar kasa dake ketare cikin babi daya na sharhi.
Dadin dadawa, takardar ta nuna cewa, dankarun kasar Sin za su yi kokarin raya aikin tsaron kasa da sojojin kasar na zamani, tare kuma da yin hadin gwiwa da kasa da kasa ta fuskar tsaro, ta yadda za su samar da wani yanayi mai kyau a duniya dangane da zaman lafiya, kwanciyar hankali, yin zaman daidai wa daida, amincewa da juna da ma kawo moriyar juna. (Amina)