Ma Zhaoxu ya ce, sabon kundin kiyaye tsaro na kasar Japan ya yi sharhin da ba gaskiya kan raya ayyukan tsaro da kasar Sin ke yi,dalilin da yasa kasar Sin ta nuna rashin jin dadinta sosai.. Kuma tana kokarin daidaita batutuwan dake faruwa a tsakanin kasa da kasa ta hanyar yin shawarwari domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a nahiyar Asiya da kuma duk duniya. Bunkasuwar kasar Sin ta samar da kyakkyawan zarafi ga kasashen duniya ciki har da kasar Japan, ba ta taba kawo barazana ga ko wace kasa ba, a da haka, nan gaba ma haka.
A game da haka, kakakin ma'aikatar tsaro ta kasar Sin Geng Yansheng ya bayyana cewa, kasar Sin ta karfafa tsarin tsaron kasa da raya rundunar soja domin tabbatar da cikakken yankin kasa da raya tattalin arziki yadda ya kamaya. Kasar Sin tana fatan kasar Japan za ta yi hangen nesa kan hulda a tsakanin kasashen biyu, da kokarin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.(Lami)